Zab 106:32-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Jama'ar Ubangiji suka sa ya yi fushi.A maɓuɓɓugan Meriba,Musa ya shiga uku saboda su.

33. Suka sa Musa ya husata ƙwarai,Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.

34. Suka ƙi su kashe arna,Yadda Ubangiji ya umarta,

35. Amma suka yi aurayya da su,Suka kwaikwayi halayen arnan.

Zab 106