Zab 106:29-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu,Mugawar cuta ta auka musu,

30. Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin,Aka kuwa kawar da annobar.

31. Tun daga lokacin nan ake ta tunawa da shi,Saboda abin da ya yi.Za a yi ta tunawa da shi a dukan zamanai masu zuwa.

32. Jama'ar Ubangiji suka sa ya yi fushi.A maɓuɓɓugan Meriba,Musa ya shiga uku saboda su.

33. Suka sa Musa ya husata ƙwarai,Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.

34. Suka ƙi su kashe arna,Yadda Ubangiji ya umarta,

35. Amma suka yi aurayya da su,Suka kwaikwayi halayen arnan.

36. Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada.Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.

37. Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.

38. Suka karkashe mutane marasa laifi,Wato 'ya'yansu mata da maza.Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana,Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.

39. Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,Suka zama marasa aminci ga Allah.

40. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa,Ransa bai ji daɗinsu ba.

Zab 106