10. “Duk da haka yawan mutanen Isra'ilaZai zama kamar yashi a bakin teku,Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba.Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
11. Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya,Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya.Za su shugabanci ƙasarGama ranar Yezreyel babba ce.”