1. Zuciyar Yunusa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan abu, har ya yi fushi.
2. Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.
3. Domin haka fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka ɗauki raina, gama yanzu gara in mutu da in zauna da rai.”
4. Ubangiji kuwa ya amsa ya ce, “Daidai ne ka yi fushi?”
5. Yunusa ya fita daga birnin, ya yi wajen gabas, ya zauna. Ya yi wa kansa rumfa, ya zauna a inuwarta, yana jira ya ga abin da zai sami birnin.