4. “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.
5. Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.
6. Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.
7. Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.
8. Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”
9. Ku sanar wa al'ummai da wannan,Su yi shirin yaƙi,Su kira mayaƙa!Su tattaro sojoji, su zo!
10. Su bubbuge allunan garmunansu,Su yi takuba da su.Su ƙera māsu da wuƙaƙen da akeyi wa itatuwa aski.Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumine!”
11. Su gaggauta, su zo su al'ummai dasuke kewaye,Su tattaru a kwarin.“Ya Ubangiji, ka saukar darundunarka mai ƙarfi.”