1. Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.
2. Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.
3. Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.
4. Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.
5. In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.