12. Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.
13. Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”