W. Yah 21:25-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ƙofofinsa kuwa ba za a rufe su da rana ba har abada, ba kuwa za a yi dare a can ba.

26. Za a kuma kawo darajar al'ummai da girmansu a gare shi.

27. Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.

W. Yah 21