W. Yah 2:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.

6. Amma a wannan waje kam ka kyauta, kā ƙi ayyukan Nikolatawa, ni ma kuwa na ƙi su.

7. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”

8. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Simirna haka, ‘Ga maganar wanda yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu, ya kuma sāke rayuwa.

9. “ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama'ar Shaiɗan ne.

10. Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.

11. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba ko kaɗan.’ ”

12. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Birgamas haka, ‘Ga maganar wanda yake da takobi mai kaifi biyu.

13. “ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.

W. Yah 2