20. Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.
21. Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.
22. To, ga shi, zan jefa ta a gado, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta.
23. Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.
24. Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al'amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.
25. Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.