W. Yah 2:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. “ ‘Na san ayyukanka, da ƙaunarka, da bangaskiyarka, da ibadarka, da jimirinka, ayyukanka kuma na yanzu, sun fi na farkon.

20. Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.

21. Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.

22. To, ga shi, zan jefa ta a gado, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta.

23. Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.

24. Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al'amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.

25. Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.

26. Duk wanda ya ci nasara, yake kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi zan bai wa iko a kan al'ummai,

27. zai kuwa mallake su da sanda ta ƙarfe, ya farfashe su kamar tukwanen yumɓu

28. (kamar yadda Ni ma kaina na sami iko a gun Ubana), zan kuma ba shi gamzaki.

29. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

W. Yah 2