W. Yah 2:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Birgamas haka, ‘Ga maganar wanda yake da takobi mai kaifi biyu.

13. “ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.

14. Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.

15. Haka kai ma kake da waɗansu masu bin koyarwar Nikolatawa.

16. Saboda haka, sai ka tuba. In ba haka ba kuwa, zan zo a gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da yake a bakina.

17. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”

18. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Tayatira haka, ‘Ga maganar Ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai ƙafafu kamar gogaggiyar tagulla.

19. “ ‘Na san ayyukanka, da ƙaunarka, da bangaskiyarka, da ibadarka, da jimirinka, ayyukanka kuma na yanzu, sun fi na farkon.

20. Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.

21. Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.

22. To, ga shi, zan jefa ta a gado, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta.

23. Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.

24. Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al'amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.

25. Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.

W. Yah 2