W. Yah 17:16-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ƙahonin nan goma kuma da ka gani, wato, su da dabbar nan za su ƙi karuwar, su washe ta, su tsiraita ta, su ci namanta, su ƙone ta,

17. domin Allah ya nufe su da zartar da nufinsa, su zama masu ra'ayi ɗaya, su bai wa dabbar nan, mulkinsu, har a cika Maganar Allah.

18. Matar nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da yake mulkin sarakunan duniya.”

W. Yah 17