W. Yah 17:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Waɗannan ra'ayinsu ɗaya ne, za su kuma bai wa dabbar nan ikonsu da sarautarsu.

14. Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”

15. Sai mala'ikan nan ya ce mini, “Ruwan nan da ka gani, a inda karuwar nan take a zaune, jama'a ce iri iri, da taro masu yawa, da al'ummai, da harsuna.

16. Ƙahonin nan goma kuma da ka gani, wato, su da dabbar nan za su ƙi karuwar, su washe ta, su tsiraita ta, su ci namanta, su ƙone ta,

17. domin Allah ya nufe su da zartar da nufinsa, su zama masu ra'ayi ɗaya, su bai wa dabbar nan, mulkinsu, har a cika Maganar Allah.

18. Matar nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da yake mulkin sarakunan duniya.”

W. Yah 17