W. Yah 14:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.

13. Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”

14. Sa'an nan na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗan Mutum a zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa.

15. Sai mala'ika ya fito daga Haikalin, yana magana da murya mai ƙarfi da wanda yake a zaune a kan gajimaren, yana cewa, “Ka sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.”

16. Sai wanda yake a zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa zuwa duniya, aka girbe amfanin duniya.

17. Wani mala'ika kuma ya fito daga Haikali a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje.

W. Yah 14