W. Yah 13:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.

2. Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.

3. Ɗaya daga cikin kawunanta, an yi masa rauni kamar na ajali, amma rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki,

4. har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa ya yi kama da dabbar nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?”

5. An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba'in da biyu.

6. Sai ta buɗe bakinta don ta saɓi Allah, ta yi ta saɓon sunansa, da wurin zamansa, da waɗanda suke a zaune a Sama.

7. Aka kuma yardar mata ta yaƙi tsarkaka, ta cinye su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma.

8. Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.

9. Duk mai kunnen ji, yă ji.

10. Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle.Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.

W. Yah 13