W. Yah 12:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya.

16. Amma ƙasa ta taimaki matar, ita ƙasar ta buɗe bakinta ta shanye kogin da macijin nan ya kwararo daga bakinsa.

17. Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.

W. Yah 12