W. Yah 10:8-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”

9. Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”

10. Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala'ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.

11. Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama'a iri iri, da al'ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”

W. Yah 10