1. Ke mafi kyau cikin matan,Ina ƙaunatacce naki ya tafi?Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi?Za mu taimake ki nemansa.
2. Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke.Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.
3. Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.
4. Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima,Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza,Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.