W. W. 6:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ke mafi kyau cikin matan,Ina ƙaunatacce naki ya tafi?Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi?Za mu taimake ki nemansa.

2. Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke.Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.

3. Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.

W. W. 6