W. W. 2:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ni fure ce na Sharon,Furen bi-rana na cikin kwari.

2. Kamar yadda furen bi-rana yake a cikin ƙayayuwa,Haka ƙaunatacciyata take a cikin sauran mata.

3. Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji,Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza.Da farin ciki na zauna a inuwarsa,Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.

4. Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa,Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.

W. W. 2