Rom 7:11-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni.

12. Domin haka Shari'a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.

13. Wato, abar nan da take tagari ta jawo mini mutuwa ke nan? A'a, ko kusa! Zunubi ne ya jawo, domin ya bayyana kansa shi zunubi ne, gama ta wurin abar nan tagari ya jawo mini mutuwa, ta dalilin umarnin nan kuma, zunubi ya bayyana matuƙar muninsa.

14. Mun dai san Shari'a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi.

15. Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi.

Rom 7