Rom 6:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka?

2. A'a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, ƙaƙa za mu ƙara rayuwa a cikinsa har yanzu?

3. Ashe, ba ku sani ba duk ɗaukacinmu da aka yi wa baftisma a cikin Almasihu Yesu, a cikin mutuwarsa aka yi mana baftismar ba?

Rom 6