34. “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”
35. “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,Har da za a sāka masa?”
36. Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.