Rom 1:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne,

4. amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu.

5. Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya,

6. a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu.

7. Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Rom 1