Neh 6:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai na mayar masa da amsa cewa, “Faufau, ba a yi wani abu haka kamar yadda ka faɗa ba, kai ne ka ƙaga wannan a zuciyarka.”

9. Gama dukansu so suke su tsoratar da mu, suna cewa, “Za su daina aikin.” Amma na yi addu'a, na ce, “Ya Allah, ka ƙarfafa ni.”

10. Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”

11. Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”

12. Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi.

Neh 6