“Za mu tanadi gurasar ajiyewa, da hadayar gāri ta kullum, da ta ranakun Asabar, da ta amaryar wata, da ta ƙayyadaddun idodi, da abubuwa masu tsarki, da hadaya don zunubi saboda yi wa jama'ar Isra'ila kafara, da dukan aiki na Haikalin Allahnmu.