Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta,