Mat 6:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.

8. Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

9. Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka,‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,A kiyaye sunanka da tsarki.

10. Mulkinka yă zo,A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.

11. Ka ba mu abincinmu na yau.

12. Ka gafarta mana laifofinmu,Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

13. Kada ka kai mu wurin jaraba,Amma ka cece mu daga Mugun.’

14. Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.

15. In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”

16. “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.

Mat 6