Mat 26:51-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

51. Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunne.

52. Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa.

53. Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala'iku goma sha biyu?

54. To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”

55. Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.

56. Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

Mat 26