1. “Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.
2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.
3. Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.
4. Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.
5. Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.