Mat 25:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.

2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.

3. Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.

4. Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.

Mat 25