Mat 24:44-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”

45. “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?

46. Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.

47. Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.

48. Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’

49. sa'an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya,

50. ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba,

51. yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”

Mat 24