1. Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,
2. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su.
3. Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”
4. An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
5. “Ku ce wa 'yar Sihiyona,Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,Mai tawali'u ne,Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6. Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu.
7. Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau.
8. Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya.
9. Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”
10. Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”