Mat 15:37-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

38. Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara.

39. Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.

Mat 15