Mat 14:33-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”

34. Da suka haye, suka sauka a ƙasar Janisarata.

35. Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka aika ko'ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya,

36. suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, iyakar waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.

Mat 14