28. Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’
29. Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.
30. Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”
31. Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa.