20. Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.
21. “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.
22. Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.
23. Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.
24. Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”