Mar 4:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

9. Sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

10. Da suka kaɗaita, masu binsa da su sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan.

Mar 4