Mar 3:31-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je.

32. Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.”

33. Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?”

Mar 3