23. Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar.
24. Farisiyawa suka ce masa, “Ka ga! Don me suke yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba?”
25. Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa'ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa?
26. Yadda ya shiga masujadar Allah a zamanin Abiyata babban firist, ya ci keɓaɓɓiyar gurasan nan, wadda bai halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?”
27. Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba.