Mar 15:45-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Da ya san haka daga bakin jarumin ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin.

46. Sai Yusufu ya sayi likkafanin lilin. Da ya sauko da Yesu, ya sa shi a likkafanin lilin ɗin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, ya kuma mirgina wani dutse a bakin kabarin.

47. Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yusufu sun ga inda aka sa shi.

Mar 15