3. Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar ƙura a ƙarƙashin ƙafafunku, a ranan nan da zan aikata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
4. “Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama'ar Isra'ila su kiyaye.
5. “Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.
6. Zai sāke kawo iyaye da 'ya'ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”