M. Sh 28:17-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “La'anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.

18. “La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku.

19. “Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita.

20. “Ubangiji zai aiko muku da la'ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.

M. Sh 28