1. Musa da dattawan Isra'ila suka umarci jama'a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau.
2. Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
3. Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku.