15. “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa.
16. Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.
17. “Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.
18. Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa'adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
19. “Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa.