M. Sh 23:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa.

16. Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.

17. “Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.

M. Sh 23