1. “Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
2. “Shege ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
3. “Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
4. domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku.
5. Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal'amu, sai Ubangiji ya juyar da la'anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.
6. Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.
7. “Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.
8. 'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”
9. “Sa'ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu.
10. Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin.
11. Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa'ad da rana ta faɗi.
12. “Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa.