M. Sh 22:6-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da 'ya'yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa 'ya'yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan.

7. Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe 'ya'yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

8. “Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.

9. “Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku.

10. “Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare.

11. “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.

12. “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.

13. “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa'an nan ya ƙi ta,

14. yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa'ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’

15. sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin.

16. Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum 'yata aure, amma ya ƙi ta.

17. Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske 'yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin 'yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan.

18. Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala,

M. Sh 22