M. Sh 22:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi.

2. Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa'an nan ku ba shi.

3. Haka nan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.

4. “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.

5. “Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

6. “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da 'ya'yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa 'ya'yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan.

7. Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe 'ya'yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

M. Sh 22